Isa ga babban shafi

Rasha ta yi ruwan makamai masu linzami kan Ukraine

Dakarun Rasha sun harba makamai masu linzami da dama kan Ukraine a wannan Alhamis a wani kazamin harin da aka kai kan ababen more rayuwa da makamashi, kwana guda bayan da Jamus da Amurka suka yi alkawarin taimaka wa Kyiv da manyan tankokin yaki. 

Ukraine ta ce, ta yi nasarar kakkabo da dama daga cikin makaman masu linzami da Rasha ta harba.
Ukraine ta ce, ta yi nasarar kakkabo da dama daga cikin makaman masu linzami da Rasha ta harba. AP - Anonymous
Talla

Shugaban rundunar sojin Ukraine Valery Zaluzhny ya ce, akalla makamai masu linzami 55 Rasha ta harba a sabon harin na wannan Alhamis, amma kuma sun yi nasarar harbo 47 daga cikin su ciki har da 20 da aka harba wa babban birnin kasar Kiev. 

Yayin da Rundunar Sojin Saman kasar  ta yi shelar nasarar kakkabo kuramen jiragen har sama da guda 24 da sojojin Rasha suka harba daga kudancin kasar ta Ukraine. 

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da Amurka ta bi sahun Jamus wajen sanar da samar wa Ukraine tankokin yaki kirar Abrams guda 31 domin taimaka mata tunkarar mamayar da Rasha ke yi, yayin da Jamus ta ce, nata samfurin tankokin yaki na 'Leopard' guda 14 za su isa Ukraine kafin karshen watan Maris. 

Tuni fadar gwamnatin Kremlin ta ce, Rasha na kallon bai wa Ukraine wadannan tankokin yakin tamkar kasashen sun shiga cikin yakin ne kai tsaye. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.