Isa ga babban shafi

Zelensky ya bukaci taimakon jiragen yaki daga Birtaniya da kawayenta

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya bukaci Burtaniya da kawayen ta da ta taimaka masa da kwarrarun sojoji, wadanda zasu yiwa sojojin kasar sa horo na musamman a ci gaba da yakin da suke yi da Dakarun Rasha.

Franministan Birtaniya Rishi Sunak lokacin da ya karbi bakwancin shugaban kasar Ukraine Volpdymyr Zelensky a Landan.
Franministan Birtaniya Rishi Sunak lokacin da ya karbi bakwancin shugaban kasar Ukraine Volpdymyr Zelensky a Landan. © AP - Andrew Matthews
Talla

A ziyarar da shugaban na Ukraine ya kai majalisar dokokin Burtaniya bayan ganawar sa da sarki Charles na biyu ya ce akwai bukatar Burtaniya ta bada tata gudunmuwa a yakin da Ukraine din ke yi da Rasha. 

Yayin da barin wuta ke ci gaba da munana a Gabashin Ukraine, Zelensky ya ce lokaci ya yi da kasashen turawa zasu taimakawa kasar da jiragen yaki da makamai masu linzami don durkusar da Rasha.

Bayan ganawar ta ‘yan Majalisar Burtaniya, kasar ta yiwa Zelensky alkawarin taimaka masa da sojoji sama da dubu 10, da kuma matuka jiragen yakin da zasu horas da na Ukraine din. 

A bayanin da Franminista kasar Rishi Sunak ya yi ya ce tabbas Burtaniya zata taimakawa Ukraine da sojoji da kayan yaki, amma ba wani al’amari bane da zai kasance nan kusa, abu ne da zai ja lokaci.  

A cewar sa a yanzu za’a tabbatar da fara horas da matuka jiragen yakin Ukraine, don basu damar tuka jiragen na zamani da kungiyar tsaro ta Nato ta samarwa kasar. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.