Isa ga babban shafi

Zelensky ya yi alkawarin murkushe dakarun Rasha a Soledar

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi alkawarin samar da "dukkan abin da ya dace" ga sojojin Ukraine  da ke fagen daga da Rasha a Soledar da Bakhmout, garuruwa biyu a gabashin kasar da Rasha ke kokarin mamayewa ko ta halin kaka don sauya yanayin yakin.

Yankin  Bakhmout, a yankin Donetsk, na kasar Ukraine
Yankin Bakhmout, a yankin Donetsk, na kasar Ukraine AP - Evgeniy Maloletka
Talla

Shugaba Zelensky ya jaddada cewa rukunin da ke kare wadannan garuruwan za a ba su da harsashi da duk abin da ake bukata cikin sauri ba tare da tsangwama ba.

 Halin da ake ciki a Soledar ya kasance mawuyaci ga sojojin Ukraine inda ake ci gaba da gwabza fada mafi muni a cewar mataimakin ministan tsaro Ganna Maliar.

Soledar da ke da ma'adinan gishiri yana da nisan kilomita 15 a arewa maso gabashi da birnin Bakhmout, da sojojin Rasha suka kwashe tsawon watanni suna kokarin kwacewa.

Ga masanin harkokin soji Anatoly Khramchikhine, kame Soledar, wani karamin gari mai kusan mutane 10,000 kafin yakin, wanda yanzu ya lalace gaba daya, zai baiwa Rasha damar samun nasarar soji, bayan jerin koma baya da sojojin Rasha suka fuskanta a baya.

A nasa bangaren Andreï Baïevskiï, dan majalisar masu rajin ballewa daga kasar Rasha a yankin Donetsk, ya jaddada a nasa bangaren cewa kama Soledar zai ba da damar  yanke layukan samar da kayayyaki na Ukraine wanda zai ba da damar kare Bakhmout.

Kakakin fadar shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov ya ce "Har yanzu akwai sauran aiki da yawa a gaba."

A cikin taswirar gabashin Ukraine da ma'aikatar tsaron Rasha ta fitar a ranar Alhamis, Soledar bai bayyana a karkashin ikon soja na Moscow ba.

Mataimakin Ministan Ganna Maliar ya nanata cewa, "Muna da tsayin daka, yana mai yabawa "jurewa da jarumtaka" na sojojin Ukraine.Kakakin rundunar sojin Ukraine Sergei Tcherevaty, ya yi ikirarin a gidan talabijin cewa, 'yan kasar Rasha na kai hare-hare akai-akai a garin Soledar, inda ya bayar da rahoton cewa, a cikin sa'o'i 24 da suka gabata an harba manyan makamai 91 a birnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.