Isa ga babban shafi

An kama Tan hudu da rabi na hodar iblis a wani tsibirin kasar Spain

'Yan sandan kasar Spain sun sanar a yau asabar da  kama tan hudu da rabi na hodar iblis a tsibirin Canaries a cikin wani jirgin ruwan dakon kaya na kasar Togo wanda ya fito daga yankin Latin Amurka.

Wasu daga cikin jami'an tsaro masu yaki da fataucin hodar ibilis
Wasu daga cikin jami'an tsaro masu yaki da fataucin hodar ibilis ASSOCIATED PRESS - Moises Castillo
Talla

Jirgin mai suna "Orión V", wanda ke jigilar shanu daga Latin Amurka zuwa kasashen gabas ta Tsakiya, an sa ido sosai fiye da shekaru biyu a kan sa.

Jami’an tsaro sun mayar da hankali a kan sa tare da gudanar da bincike na musaman,duk da wannan kokari ba a samun kwayoyi a cikin sa ba, in ji 'yan sanda.

A karshe jami’an tsaro sun bayyana cewa wata na'urar "jikin jirgin ruwa" ta ba da damar a ranar talata 24 ga watan Janairu don kama hodar iblis din da aka boye a cikin silo da ya kamata a yi amfani da shi wajen ciyar da dabbobi.

Aikin, wanda ya hada da wasu jami’an  hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Amurka DEA, cibiyar gudanar da bincike ta kasa da kasa kan binciken leken asirin ruwa a teku (MAOC-N), da hukumomin Togo da kuma 'yan sandan Spain, ya sa aka kama ma'aikatan jirgin su 28. , na kasashe tara daban-daban.

Jirgin ruwan mai sunan "Orión V", wanda ke amfani da tutar kasar Togo, yana da girma iri daya da wani jirgin kasar Togo da aka kama a tsakiyar watan Janairu a wannan yanki mai nisan mil 62 kudu maso gabas da tsibiran Canaries, jirgin mai suna "Blume", wanda a cikin sa an samu adadin hodar iblis iri daya.

Don haka jimilar tan tara na kwayoyi ne aka kama a watan Janairu, in ji ‘yan sandan a cikin wata sanarwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.