Isa ga babban shafi
Argentina

Hodar Ibilis Ta Kashe Mutane 12 a Argentina, Wasu 50 na Asibiti

A kasar Argentina mutane 12 suka gamu da ajalinsu bayan da suka sha gurbatacciyar tabar ibilis Koken (Cocaine) wasu 50 kuma na cikin wani hali a asibiti dake birnin Buenos Aires.

Wani asibiti dake Argentina
Wani asibiti dake Argentina AFP/Archivos
Talla

Majiyoyin samun labarai na cewa Hukumomin kasar na tsare da mutane 10 da ake tuhuma da gurbata tabar ibilis din da tayi ajalin mutane 12.

‘Yan sandan yankin ne suka kai samame inda suka rutsa mutane da ke da hannu  wajen saida hodar ibilis din.

A cewar Jami'an tsaro har yanzu basu gano abinda aka gurbata hodar ibilis din da shi ba.

Jami'an sun gargadi mutanen da suka sayi hodar ibilis daga yankin dan tsakanin nan da kada su kurkura su yi amfani da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.