Isa ga babban shafi
Colombia

Kasurgumin mai safarar hodar Ibilis na duniya ya shiga hannu a Colombia

Jami’an tsaron Colombia sun samu nasarar cafke kasurgumin mai fataucin muggan kwayoyi mafi shahara da aka fi sani da Otoneil, wanda suka dade suna farautarsa, la’akari da cewar a halin yanzu shi ke kan gaba wajen safarar hodar iblis a duniya.

Kasurgumin mai fataucin muggan kwayoyi mafi shahara da aka fi sani da Otoneil bayan kama shi a kasar Colombia.
Kasurgumin mai fataucin muggan kwayoyi mafi shahara da aka fi sani da Otoneil bayan kama shi a kasar Colombia. AFP - HANDOUT
Talla

Bayanan hukumomin tsaro sun ce an kama Otoniel da asalin sunansa shi ne Dairo Antonio Usuga, a kusa da daya daga cikin manyan ofisoshinsa a yankin Necocli, dake kusa da kan iyaka da Panama.

Sojoji akalla 500 tare da jirage masu saukar ungulu 22 gami da taimakon hukumomin tsaron Ingila da Amurka ne suka kai samamen da ya basu nasarar cafke Otoniel a yankin Necocli, inda a kokarin hakan dan sanda 1. ya rasa ransa.

Hotunan da gwamnati ta fitar sun nuna Otoniel mai shekaru 50 cikin ankwa yayin da kuma sojoji ke kewaye shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.