Isa ga babban shafi

William ya zama Yarima mai jiran gadon sarautar Birtaniya

Bayan nadin mahaifinsa a matsayin sarkin Ingila, Yarima William zai zama mai jiran gadon sarautar kasar lamarin da ke nuna nauyi zai karu akansa wajen rungumar ayyukan masarauta sabanin a baya musamman bayan kaucewar dan uwansa Yarima Harry da kuma kawunsa Yarima Andrew.

Yarima William, mai jiran gadon Sarautar Birtaniya.
Yarima William, mai jiran gadon Sarautar Birtaniya. AP - Adrian Dennis
Talla

William wanda ya girma da cikakken sanin iya kasancewa sarkin Ingila a wani lokaci, shi ke dauke da nauyin ilahirin ayyukan Masarauta bayan ficewar dan uwansa Harry.

Masu sharhi na ganin William na da sa’ar iya dadewa a karagar mulkin Birtaniya, fiye da mahaifinsa wanda ke karbar sarauta y ana da shekaru 73 a Duniya bayan mutuwar mahaifiyarsa sarauniya Elizabeth ta 2 mai shekaru 96.

A zantawar kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da Farfesa Robert Hazell masanin ayyukan masarauta na jami’ar College da ke birnin London ya ce bayan nadin na yanzu, Yarima William mai shekaru 40 wanda tuni ya ke aiki da Sojin kasar zai karbi wasu karin ayyukan masarauta wanda a baya mahaifinsa ke tafiyarwa.

William da ke sahun fitattun iyalan sarautar Birtaniya da suka yi kaurin suna kuma suke da matukar farin jini ga al’ummar kasar yanzu haka shi da matarsa Katherine za su zamo Yarima da Gimbiyar Cornwall sabanin Yarima da Gimbiyar Duke da su ke a baya.

Marubucin Masarauta, Phil Dampier ya ce tun daga haihuwar William a ranar 21 ga watan Yunin 1982 kaddara ta bayyana shi a matsayin wanda zai zama sarkin Ingila a gaba bayan gushewar mahaifinsa da yanzu ya karbi ragamar sarautar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.