Mutuwar sarauniya Elizabeth ta 2 ta tilasta dakatar da wasanni a Ingila
Masu kula da gasar tseren doki a Ingila sun sanar da dakatar da ilahirin wasannin gasar sakamakon mutuwar Sarauniya Elizabeth ta 2, a yayinda wasan cricket da za a buga tsakanin Ingila da Afrika ta Kudu shi ma aka dakatar.
Wallafawa ranar:
Dukkannin wasanni tsere na Juma’ar nan da kuma wasannin Cricket na gasar Heyhoe Flint an soke biyo bayan mutuwar ta Queen Elizabeth ta 2 a yammacin jiya alhamis.
Haka zalika ba za a yi wasannin gasar kwallon Golf na gasar PGA Championship da ke gudana a wannan Juma’a ba.
Hukumar gasar Firmiyar Ingila ma ta daktar da dukkannin wasannin da jadawali ya nuna za a buga su a wannan Juma’a.
Sarauniya Elizabeth na 2, wadda basarakiyar Birtaniya mafi dadewa a kan karaga, ta rasu tana da shekasru 96, bayan da ta shafe shekaru 70 tana mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu