Isa ga babban shafi
Tennis

Matsanancin zafi ya sa an dakatar da wasannin Australian Open

An dakatar da wasannin da ake fafatawa a gasar Tennis ta Australian Open saboda matsanancin zafi inda maunin ya haura maki 43 na Celsius a yau Alhamis rana ta uku da zafin ya fi tsananta. Tun a ranar Talata masu shirya wasannin ke fuskantar suka saboda yadda suke tursasawa ‘yan wasa su fafata a cikin zafi.

Maria Sharapova tana gasa kanta da kankara saboda matsanancin zafi a lokacin da ta ke karawa da ta Karin Knapp a gasar Tennis ta Autralian Open
Maria Sharapova tana gasa kanta da kankara saboda matsanancin zafi a lokacin da ta ke karawa da ta Karin Knapp a gasar Tennis ta Autralian Open REUTERS/David Gray
Talla

Masu shirya wasannin sun ce ko za’a dawo filin wasannin na Tennis sai da misalin karfe 5 na yamma.

A cikin zafin ne dai ‘Yar wasan Rasha Maria Sharapova ta sha da kyar a yau Alhamis a karwarta da Karin Knapp ta Italia. Idan an jima ne kuma Rafael Nadal na Spain ake sa ran zai fafata tsakanin shi da Thanasi Kokkinakis dan kasar Australia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.