Venus da Errani sun sha kashi a Australian Open
Li Na ta China ta samu nasarar tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar Australian Open da aka bude a Melbourne bayan ta doke Ana Konjuh ta Croatia, amma tun a tashin farko an yi waje da Venus Williams ta Amurka da Sara Errani ta Italia.
Wallafawa ranar:
A yau litinin ne aka bude wasannin gasar Australian Open daya daga cikin manyan gasannin Tennis a Duniya.
Venus ta Amurka ta sha kashi ne a hannun Ekaterina makarova ta Rasha. Venus Williams sau bakwai tana lashe kofunan manyan gasar Tennis na Gram Slams amma rabon ta lashe kofi tun a 2008.
Sara Errani ta Italia ta sha kashi ne ci 6-3, 6-2 tun a tashin farko a karawarta da ‘Yar wasan Jamus Julia Goerges.
A gobe ne mai rike da kofin gasar a bangaren Mata Victoria Azarenka zata fara haskawa a Australian Open.
A bangaren Maza David Ferrer da Stanislas Wawrinka da Tomas Berdych da Richard Gasquet dukkaninsu sun tsallake zuwa zagaye na biyu bayan sun samu nasara a wasanninsu na farko.
Yanzu haka dai ana gudanar da wasannin ne cikin matsanancin zafi a Australia inda ma’aunin ya kai maki 40 na Celsius. Mahukuntan wasan sun yi gargadi ga ‘yan wasan wajen kaucewa shan barasa da ke duma jiki don tsira da rayuwarsu a lokacin wasannin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu