Isa ga babban shafi
Tennis

Djokovic ya lashe gasar Paris Masters

Novak Djokovic ya lashe gasar Paris Masters bayan ya doke David Ferrer da ci 7-5, 7-5 a wasan karshe na gasar da aka kammala a jiya Lahadi a filin wasa na Bercy Arena. 

Novak Djokovic a lokacin da ya lashe gasar Paris Masters
Novak Djokovic a lokacin da ya lashe gasar Paris Masters RFI/Pierre René-Worms
Talla

Ferrer ya kasance dan wasan Tennis na farko da ya kasa kare kofin wannan gasa yayin da Djokovic ke hangen kwato matsayi na daya da Rafael Nadal ya karbe a hnunshi yayin da suke shirin karawa gasar duniya ta London da za a fara a wannan makon.

Har ila yau wannan nasara na nufin Djokovic shine dan wasan Tennis 15 a duniya da ya lashe gasa 40 a rayuwarshi ta wasan tennis.

“Ina mai matukar farin ciki a yanzu, wannan shine mako mafi girma a wannan kakar wasa.” Inji Djokovic.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.