Isa ga babban shafi
Tennis

Nadal da Azarenka sun lashe kofin Cincinnati

Victoria Azarenka ta lashe kofin Cincinnati bayan ta doke Serena William a wasan da suka kwashe tsawon sa’o’I biyu da rabi suna fafatawa. ‘Yan wasan biyu suna cikin jaruman da ake ganin zasu iya lashe babbar gasar Tennis din da karowata ta US Open a bana.

Victoria Azarenka ta Belarus tana murna bayan ta doke Serena a wasan karshe da suka fata a gasar Cincinnati Open
Victoria Azarenka ta Belarus tana murna bayan ta doke Serena a wasan karshe da suka fata a gasar Cincinnati Open REUTERS/John Sommers
Talla

Wannan ne karo na biyu da Serena ke shan kashi a hannun Azarenka a bana bayan ta lashe Qatar open.

A Bangaren Maza, Rafael Nadal ne ya lashe kofin gasar na Cincinnati bayan ya doke John Isner, wanda hakan ya bashi damar kasancewa a matsayin na biyu a Duniyar Tennis. Nadal yanzu yana da jimillar kofuna 9 a bana

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.