Isa ga babban shafi
Tennis

Bartoli ta yi ritaya daga Tennis

Jarumar Tennis din kasar Faransa Marion Bartoli da ta lashe kofin Wimbledon ta bayar da sanarwar yin ritaya ta bazata daga harakar wasanni tana da shekaru 28 Wannan kuma na zuwa ne duka makwanni shida da ta doke Sabine Lisicki ta Jamus a wasan karshe na Wimbledon wanda shi ne kofinta na farko a manyan gasanni Tennis.

Marion Bartoli 'Yar wasan Tennis ta Faransa da ta lashe kofin Wimbledon
Marion Bartoli 'Yar wasan Tennis ta Faransa da ta lashe kofin Wimbledon Reuters/Thomas Lovelock/AELTC/Pool
Talla

Bartoli, tace ta dauki matakin ne saboda rauni, musamman bayan ta sha kashi a hannun ‘Yar wasan kasar Romania Simona Helep a gasar Cincinnati Masters.

“Lokaci ya yi da zan yi ritaya” inji Bartoli, kuma sanarwar na zuwa ne duka makwanni biyu a fara gasar US Open a birnin New york na kasar Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.