Isa ga babban shafi
Tennis

Nadal ya lashe kofin Montreal Masters

Rafael Nadal ya lashe kofin Montreal Masters a Canada bayan ya lallasa Milos Raonic ci 6-2, 6-2 a wasan karshe da aka gudanar a jiya lahadi Wannan kuma wani shiri na musamman da dan wasan ya yi domin lashe babban kofin gasar US Open da za’a fara a mako mai zuwa.

Rafael Nadal yana murnar lashe kofin Rogers Cup a Montreal kasar Canada
Rafael Nadal yana murnar lashe kofin Rogers Cup a Montreal kasar Canada REUTERS/Christinne Muschi
Talla

Wannan ne kuma karo na 25 da Nadal ke lashe irin wannan kofi amma kofinsa na 58 ke nan. A bana kuma Nadal ya lashe kofuna 8.

A bangaren mata kuma Serena Williams ita ce ta lashe gasar Rogers Cup da aka gudanar a Toronto, bayan ta doke Sorana Cirstea 6-2, 6-0. Inda ita ma wannan tamkar shiri ne domin shiga gasar US Open bayan ta sha kashi tun a zagayen Kwata Fainal a Wimbledon bayan ta lashe Rolland Garros a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.