Isa ga babban shafi
Tennis

Serena ta fice Wimbledon

Serena Williams Jarumar Tennis ta Duniya ta fice gasar Wmbledon bayan ta sha kashi a hannun ‘Yar kasar Jamus Sabine a zagaye na hudu. Inda bayan kammala wasan sai da Lisicki ta barke da kuka, saboda farin ciki.

'Yan wasan Tennis Serena Williams a filin wasan gasar Wimbledon bayan ta sha kashi
'Yan wasan Tennis Serena Williams a filin wasan gasar Wimbledon bayan ta sha kashi REUTERS/Toby Melville
Talla

Serena dai tana cikin jaruman da ake ganin zasu iya lashe kofin Wimbledon a bana amma ‘Yar wasan ta bi sahun Maria Sharapova da Victoria Azarenka da suka fice.

Lisicki, karo uku tana zuwa zagayen kwata Fainal a Wimbledon, kuma wannan kamar ita ce babbar nasarar da za’a ce ‘yar wasan zata yi alfahari bayan lallasa Serena 6-2, 1-6, 6-4.
Daga cikin wadanda suka tsallake zuwa zagayen kwata Fainal akwai Li Na ta China wacce ta lallasa Roberta Vinci ta Italia 6-2, 6-0.

A bangaren maza kuma David Ferrer ya tsallake zuwa zagayen Kwata Fainal karo na biyu a jere bayan ya doke dan kasar Croatia Ivan Dodig.

Anan gaba dai David Ferrer na Spain zai iya haduwa da dan wasan Argentina Juan Martin del Potro ko kuma Andreas Seppi na Italiya.

David Ferrer da Rafeal Nadal ne suka fafafata a wasan karshe na Rolland Garros, Kuma ana ganin Farrer zai iya farautar lashe Wimbledon a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.