Isa ga babban shafi
Tennis

Jaridun Birtaniya sun karrama Murray

Nasarar Andy Murray a gasar Wimbledon a Birtaniya ne ya mamaye kanun labaran Jaridun kasar inda suka bukaci a karrama shi bayan lashe kofin gasar da suke yunwa tsawon shekaru sama da Saba’in.

Andy Murray na birtaniya wanda ya lashe kofin Wimbledon a 2013
Andy Murray na birtaniya wanda ya lashe kofin Wimbledon a 2013 REUTERS/Toby Melville
Talla

Jaridar The Times tace Murray ya cancanci samun sarauta a fadar Sarauniya inda Jaridar ta nuna wani wagegen hoton dan wasan kewaye da ‘Yan kallo, tare da kanun labari mai taken “Yaro mai tarihi”.

Jaridar Daily Mail kuma saurautar ta ba Andy Murray inda ta buga kanun labarinta mai Teken “Sir Andy” dauke hoton Murray yana sumbatar kofin Wimbledon da ya lashe.

Taken Jaridar Daily Telegraph kuma shi ne, “Bayan shekaru 77, yanzu kam jira ya kare”.

Jaridar Daily Mirror kuma ta buga Takenta ne “Tarihi ya dawo hannun Murray”.

Duk da cewa Novak Djokovic ya sha kashi a gasar Wimbledon a hannun Andy Murray da aka kammala a jiya Lahadi, amma har yanzu shi ne na daya a duniyar Tennis.

Andy Murray ya kasance dan kasar Birtaniya na farko da ya lashe kofin gasar tsawon shekaru 77 da suka gabata.

Bayan kammala gasar Wimbledon Andy Murray shi ne na biyu a duniya. David Ferrer na uku , Rafael Nadal ne a matsayin na hudu, Roger Federer kuma a matsayi na Biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.