Isa ga babban shafi
Tennis

Nadal da Serena sun haska a US Open

Rafael Nadal da Serena Williams da ake ganin zasu iya lashe kofin gasar US Open dukkaninsu sun lashe wasanninsu na farko, yayin da kuma ruwa ya haifar da tsaiku a karawar Roger Federer.

Serena Williams A lokacin da ta ke karawa a gasar US Open
Serena Williams A lokacin da ta ke karawa a gasar US Open REUTERS/Ray Stubblebine
Talla

Nadal dai ya doke dan wasan Amurka ne Ryan Harrison, Yayin da kuma mai rike kofin gasar a bangaren Mata Serena Williams, ta casa ‘Yar wasan Italiya Francesca Schiavone, 6-0, 6-1.

Venus William kuma yayar Serena ita ma ta tsallake zuwa zagaye na biyu bayan ta doke Kirsten ta Belgium 6-1, 6-2.

A yau ne zakaran Tennis na Duniya Novak Djokovic zai fara haskawa a gasar inda zai kara da dan kasar Lithuania Ricardas Berankis, Roger Federer kuma zai fafata ne da Grega Zemlja.

Akwai kuma wasa tsakanin Petra Kvitova da Misaki Doi, Caroline Wozniacki zata kara ne Duan Ying-Ying ta China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.