Isa ga babban shafi
Tennis

An bude gasar US Open

A yau Litinin ne aka bude babbar Gasar Tennis ta US open, kuma akwai zaratan Tennis da za su haska a rana ta farko, inda Rafael Nadal da Roger Federer da kuma Serena Williams mai rike da kofin a bangaren Mata dukkaninsu za su haska a rana ta farko.

Agnieszka Radwanska  tana karawa da Silvia Soler a gasar US Open
Agnieszka Radwanska tana karawa da Silvia Soler a gasar US Open REUTERS/Mike Segar
Talla

Serena tana neman kare kambunta ne inda ta ke neman lashe kofi na 17 a manyan gasannin Tennis, Wimbledon da Rolland Garros da Australian Open amma kofi na Biyar take neman lashe wa a gasar US open.

Serena za ta fara karawa ne tsakaninsta da Francesca ta Italia.

Rafael Nadal na Spain wanda ya lashe kofin Rolland Garros sau Bakwai a jere zai fara fafatawa ne tsakanin shi da dan wasan Amurka Ryan Harrison, Yayin da kuma Roger Federer zai kara da Grega Zemelja na Slovenia.

Akwai kudi Dalar Amurka sama da Miliyan uku ga duk wanda ya lashe kofin gasar a bana zai karba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.