Isa ga babban shafi
Australian Open

Djokovic da Serena sun samu nasara a zagaye na biyu

Novak Djokovic na Serbia mai rike da kofin gasar Australian Open ta Tennis a yau Laraba ya tsallake zuwa zagaye na uku bayan ya doke Dan wasan Argentina Leonardo Mayer 6-0, 6-4, 6-4. Haka ma David Ferrer na Spain ya samu nasarar wasan shi a ranar Laraba inda ya doke Adrian Mannarino na Faransa.

Djokovic a gasar Australian Open
Djokovic a gasar Australian Open REUTERS/David Gray
Talla

A Bangaren Mata, Serena William Jarumar Tennis ta duniya da ke harin lashe kofin gasar sau 6 ta tsallake zuwa zagaye na uku bayan ta doke ‘Yar wasan Serbia Vesna 6-1, 6-2.

A gobe Alhamis ne Victoria Azarenka da Maria Sharapova zasu buga wasanninsu domin neman tsallakewa zuwa zagaye na uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.