Isa ga babban shafi

Masarauta ta tabbatar da Charles na 3 a matsayin sarkin Ingila na 111

Sarki Charles na 3 ya karbi rantsuwar kama aiki yau asabar a matsayin sarkin Ingila na 111 bayan da majalisar nadin sarki ta Birtaniya ta amince da cancantarsa.

Sarki Charles na 3 bayan rantsuwar kama aiki a matsayin sarkin Ingila na 111.
Sarki Charles na 3 bayan rantsuwar kama aiki a matsayin sarkin Ingila na 111. © AP - Victoria Jone
Talla

Nadin na Sarki Charles da ake haskawa kai tsaye ta gidajen talabijin a sassan Duniya na gudana a fadar St George da ke birnin London, bikin da ke zuwa gabanin jana’izar Sarauniya Elizabeth ta 2 da ta mutu ta na da shekaru 96.

Sanarwar da Majalisar masarautar ta fitar ta ce, ‘‘cikin girmama ta tabbatar da nadin Sarki Charles na III a matsayin magajin Sarauniya Elizabeth’’.

Bayan tabbatar da nadin an gudanar da harbe-harben al’ada don girmama sabon sarkin tare da fadin kalmomin fatan alkhairi daga ilahirin al’ummar kasar da ke ci gaba da fadin ‘‘Allah ya taimaki Sarki’’

A jawabin da ya gabatar yau asabar bayan tabbatar da nadin nasa Sarki Charles na III mai shekaru 73 ya ce yana sane da nauyi da kuma dawainiyar da ke kansa, kuma a shirye ya ke ya yi aiki tukuru ga al’ummar Birtaniya kamar mahaifiyarsa.

A jawabin sabon sarkin ya bayyana cewa ranar jana’izar Sarauniya Elizabeth za ta kasance cikakkiyar ranar hutu ba tare da bude kowanne sashen hada-hada ba a ilahirin sassan kasar, ko da ya ke bai sanar da rabar da aka shirya za a yi jana’izar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.