Isa ga babban shafi

Shugabannin Afrika na jimamin mutuwar Sarauniyar Ingila

Shugabannin Afrika na ci gaba da jimamin mutuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu wadda ta yi bankwana da duniya a yammacin jiya Alhamis tana da shekaru 96 bayan fama da rashin lafiya.

Marigayiya Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu.
Marigayiya Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu. © AP Photo/Alberto Pezzali
Talla

A yayin gabatar da sakon ta’aziyarsa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, tarihin Najeriya ba zai cika ba, ba tare da duba babin Sarauniya Elizabeth ba, yana mai bayyana ta a matsayin jajirtacciyar shugaba.

Shugaban Kungiyar Kasashen Afrika AU kuma shugaban Senegal, Macky Sally ya kwatanta Sarauniya Elizabeth a matsayin abar koyi, inda kuma ya ce, yana mika ta’aziyarsa cikin raunanniyar zuciya ga gwamnatin Birtaniya.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana Sarauniyar a matsayin wadda ta sadaukar da kanta wajen hidimta wa al’ummar duniya, yayin da zababben shugaban kasar ta Kenya, William Ruto shi ma ya yi jinjina ga marigayiyar musamman kan rawar da ta taka a kasashe renon Ingila.

Shi ma shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya mika sakon ta’aziyarsa da al’ummar Birtaniya, yana mai yi mata addu’ar mutuwa ta zama hutu a gare ta.

Shugaban Gabon, Ali Bongo shi ma ba a bar shi a baya ba wajen nuna alhininsa kan mutuwar Sarauniyar wadda ya bayyana ta a matsayin aminiya ga nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.