Isa ga babban shafi

Sarki Charles na III zai gabatar da jawabin farko ga al'ummar Ingila

Kowanne lokaci a yau juma’a ake saran Sabon Sarkin Ingila Charles na III ya gabatar da jawabi kan rantsar da shi a matsayin sarki da kuma makokin mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth ta II wadda ta mutu a yammacin jiya alhamis, dai dai lokacin da ya ke shirin fara aiki gadan-gadan a ranar farko ta kasancewarsa sarki.

Sarki Charles na III da zai maye gurbin sarauniya Elizabeth ta II.
Sarki Charles na III da zai maye gurbin sarauniya Elizabeth ta II. AP - Alastair Grant
Talla

Duk da ya ke ba za a haska jawabin sabon sarkin na 111 ta kai tsaye ba, bayanai sun ce za a saki jawabin Sarki Charles da yammacin yau juma’a a gidajen talabijin na sassan Duniya.

Kwanaki 10 aka tsara za a gudanar da bukukuwa hade da alhini rasuwar sarauniya da kuma nadin Sarki Charles.

Charles mai shekaru 73 shi ne basarake mafi daukar tsawon lokaci ya na dakon kujerar sarautar Ingila gabanin rasuwar mahaifiyarsa jiya a fadarta da ke Balmoral a Scotland, bai samu zarafin komawa London ba har a safiyar yau juma’a.

Wata sanarwar fadar Buckingham, ta ruwaito Sarki Charles na III na cewa ‘‘a irin wannan lokaci na alhini da tashin hankali a matsayinmu na iyalan gidan sarauta za mu samu kwanciyar hankali ne kadai bisa sanin kima da darajar sarauniya a fadin duniya lokacin rayuwarta’’.

Sarauniya Elizabeth na matsayin mafi dadewa kan mulki a tarihin sarautar Ingila, ta yadda galibin al’ummar da ke raye a yanzu basu san wani ko wata da ta kujerar ba bayan ita.

Dukkanin sassan Duniya na ci gaba da jinjinar ban girma tare da alhinin mutuwar sarauniyar hatta a kasashen Rasha da China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.