Sarauniya Elizabeth a karo na farko bata halarci bikin bude majalisar Birtaniya ba
A karon farko cikin shekaru kusan 60 sarauniyar ingila bata samu halartar bikin bude majalisar dokokin kasar ba inda ta wakilta magajin ta yarima Charles wanda hakan ke nuna cewa sannu a hankali ta fara sakar masa nauyin mulkin daya rataya a wuyanta.
Wallafawa ranar:
Sarauniyar, ’yar shekaru 96 da haihuwa bisa al’ada ita ke jagorantar bikin zaman bude majalisar inda zata jaddada kodurori da dokin gwamnatin ta.
Fadar Buckingham a sanarwar data batar ta shaida cewa sarauniyar bazata samu halartar babban taron ba bisa shawarwarin likitaci ,saboda gudun matsaloli na lafiya dake da alaka da zirga-zirga.
Wannan lamari na nuna gajiya saboda yawan shukaru ,bayan kwashe shekaru 70 kan karagar mulki.
Yariman Wales Charles dake wakiltan sarauniyar yaje taron da babban dansa yarima Williams wanda shine na biyu a jerin masu jiran gadon kujerar sarautar.
Sarauniya ingilan ta rage fita taruka tun bayan kwanciya na kwana guda da tayi a asibiti a watan octoban daya gabata, kuma a lokuta da dama tasha korafin kan jimawa a tsaye ko tariyar kafa maid dan tsawo,kuma baya ga hakan tayi fama da cutar korona a watan febrairun daya gabata.
Sau biyu kawai ta taba fashin babban taro a 1959 da 1963,lokacin da take da cikin yarima Andrew da yarima Edward.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu