Isa ga babban shafi
Birtaniya

Mawaka sun cashe domin karrama Sarauniya Elizabeth ta Birtaniya

Mawaka sun gudanar da kade kade da raye raye, a gaban daruruwan mutane a birnin London, da suka hada da Robbie Williams da Elton John da Stevie Wonder domin karrama Sarauniyar Ingila ta Biyu da ke bukin cika ashekaru 60 saman karagar mulki.

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta Biyu tana ran gadi dogaran Birtaniya.
Sarauniyar Ingila Elizabeth ta Biyu tana ran gadi dogaran Birtaniya. REUTERS/Andrew Winning
Talla

Sai dai an gudanar da bukin, ba tare da Yarima Philips ba mai shekaru 91 na haihuwa, saboda rashin lafiyar da ya kamu da ita, wanda aka ruga da shi zuwa asibiti.

A yau Talata ne za'a kammala bukin Sarauniya Elizabeth ta Biyu bayan kwashe kwanaki Hudu ana cashewa a Birnin London.

Kafafofin yada labaran Birtaniya sun jinjinawa Sarauniya Elizabeth a kokarinta na halartar bukin duk da rashin lafiyar Mijinta. Kamar yadda Jaridun kasar; Daily Telegraph da Daily Mail da Daily Express suka buga babban Labari mai taken: “za’a ci gaba da buki".

Sama da mutane 10,000 ne suka samu halartar bukin mawaka da aka gudanar a fadar Buckingham.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.