Isa ga babban shafi
Birtaniya

Sarauniya Elizabeth na bikin cika shekaru 90 a duniya

Al’ummar Birtaniya na bikin cika shekaru 90 da haihuwar Sarauniya Elizabeth ta biyu, wanda zai kunshi ziyarar ban girma daga Firaminista David Cameron wanda zai jagoranci ‘Yan Majalisar kasar a yau Alhamis.

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II
Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II REUTERS
Talla

Yarima Charles zai gabatar da jawabin girmama ta kafar rediyo da za a watsa.

Ana sa ran Sarauniyar wadda bara ta doke kakar kakarta a matsayin Sarauniyar da tafi kowacce dadewa kan karagar mulki a kasar, za ta gudanar da wani kwarya kwaryar biki a Windsor Castle da kuma liyafar cin abinci tare da iyalan gidan sarautar kasar.

Ana kuma sa ran sojojin Birtaniya za suyi bikin harba bindigogi domin girmama Sarauniyar a birnin London.

Tun a ranar Laraba masoya suka hada gangami a Windsor dauke da Tutar Birtaniya suna taya Sarauniya murnar ranar haihuwarta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.