Sarauniya Elizabeth mai dogon zamani a Ingila
Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu na daf da kafa sabon tarihi a kasar a matsayin Sarauniyar da tafi dadewa kan gadon sarautar Ingila a ranar 9 ga watan Satumba mai zuwa.
Wallafawa ranar:
Wannan zai bai wa Sarauniyar mai shekaru 89 a duniya damar zarce kakarta Sarauniya Victoria da ta kwashe shekaru 63 akan karagar mulki daga shekarar 1837 zuwa 1901.
Sarauniya Elizabeth ta yi zamani da Firaminista na farko a India Jawaharlal Nehru da kuma zamanin Janar Charles de Gaulle na Faransa.
A 1952 ne Elizabeth ta zama Sarauniyar Ingila bayan mutuwar Mahaifinta Sarki George na shida wanda ya mutu yana da shekaru 56 a duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu