Mutuwar Sarauniya
Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta mutu tana da shekaru 96
Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta mutu tana da shekaru 96 a wannan yammaci na Alhamis kamar yadda fadarta ta Buckingham ta sanar, yayin da tuni shugabannin kasashen duniya suka fara aike wa ta sakwannin ta’aziyar rashinta.
Wallafawa ranar:
Talla
Sarauniya Elizabeth ita ce basarakiyar da ta fi jimawa kan karagar mulki a tarihin Birtaniya, inda ta gaji karaga daga mahaifinta a shekara ta 1952.
Yanzu haka babban danta Yarima Charles mai shekaru 73, shi ne zai gaji gadon mulkin Ingila kamar dai yadda yake a al’adance.
Za mu kawo muku karin bayani nan gaba…
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu