Isa ga babban shafi

Erdogan ya bukaci Sweden ta kawo karshen goyon bayan 'yan ta'adda

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bukaci Firaministan Sweden Magdalena Andersson da ta dauki kwararan matakai don kawo karshen tallafin kudi da siyasa ga kungiyoyin 'yan ta'adda.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan REUTERS - YVES HERMAN
Talla

Fadar gwamnatin Turkiya tace, Erdogan ya shaidawa Andersson ta wayar tarho cewa "dole ne a kawo karshen tallafin siyasa, kudi da makamai da Sweden ke baiwa kungiyoyin 'yan ta'adda."

Turkiyya ta yi barazanar toshe yunkurin kasashen Sweden da Finland na zama mamba a kungiyar tsaro ta NATO, tana mai zargin kasashen biyu da marawa haramtacciyar jam'iyyar Kurdawa ta (PKK) baya da Ankara da kawayenta na yammacin Turai suka sanya a cikin jerin kungiyoyin ta'addanci.

Erdogan ya ce, Turkiyya na fatan kasar Sweden ta dauki kwararan matakai na nuna damuwa na goyon bayan Ankara kan 'yan ta'addar PKK kamar takwarorinsu dake Iraki da Siriya.

Yunkurin mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a watan Fabrairu ya sauya ra'ayin siyasa a dukkan kasashen Nordic domin shiga cikin kawancen sojojin kasashen yammacin Turai.

Samun dama shiga NATO na buƙatar amincewar duk membobi 30 da ke ciki,  kuma da alama Turkiyya na neman kawo cikas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.