Isa ga babban shafi
Zaben Faransa

Zaben Faransa- Tarihin Fabien Roussel dan takarar shugaban kasa

A ci gaba da takaitattun tarihin 'yan takarar neman kujerar shugabancin kasar Faransa da mu ke kawo muku, yau muna dauke da tarihin dan takara Fabien Roussel dan siyasar da zai shiga zaben na wannan wata karkashin jam'iyyar kwamunisanci mai ra'ayin burguzu.

Fabien Roussel dan takarar kujerar shugabancin Faransa karkashin jam'iyyar kwaminisanci.
Fabien Roussel dan takarar kujerar shugabancin Faransa karkashin jam'iyyar kwaminisanci. © RFI/Pierre René-Worms
Talla

An haifi Fabien Roussel ne a lardin Béthune na kasar Faransa a ranar 16 ga watan aprilun shekarar 1969, a lokacin karatunsa ne a Champigny-sur-Marne ya shiga kungiyar matasa 'yan kwaminisancin Faransa (MJCF).

Dan jaridar ne mai daukar hoton kyamara, ya yi aiki karkashin Michelle Demessine, a lokacin ya na rike da mukamin sakataren kasa a gwamnatin Leonel Jospin. 

Tarihin wannan dan atakara a fagen siyasa ya fara ne, a lokacin zaben kananan hukumomi na shekarar 2014 inda aka zabe shi Kansilar Saint-Amand-les-Eaux.

A lokacin zaben majalisar dokokin 2017, an zabe shi kan kujerar dan majalisar dokoki na mazabar ta 20 ta arewa, inda ya canji Alain Bocquet, magajin garin Saint-Amand-les-Eaux haka kuma mamba a jam’iyyar kwamunisancin ta Faransa.

A watan Oktoban 2018, magoya bayan jam’iyar kwamunisanci sun zabi Fabien Roussel kan mukamin babban sakataren jam’iyar na kasa.

Fabien Roussel ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar neman kujerar shugabancin kasar ne a shekarar 2022 bayan da a ranar 13 ga watan Maris 2021, Jam’iyasa ta amince da takararsa.

A wani hasashe da cibiyar Ispos-Sopra Steria ta gudanar domin tashoshin Radio France da France Télévisions a ranar lahadi 27 ga watan yunin 2021, ya nuna cewa kimanin 2,5% na yan kasar ta faransa ne ke da aniyar kada masa kuri’a a zaben da za a gudanar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.