Isa ga babban shafi
Faransa-Zaben Faransa

Zaben Faransa: Tarihin Anne Hidalgo 'yar takarar shugaban kasa

Anne Hidalgo ta jam'iyyar 'yan gurguzu wato (Socialist Party) na cikin 'yan takara 12 da za su fafata da juna a babban zaben Faransa na watan nan wanda a cikinsu kasar za ta fitar da shugaban ta na gaba da zai ja ragamarta zuwa shekaru 5 masu zuwa.

Anne Hidalgo 'yar takarar shugabancin kasa a Faransa.
Anne Hidalgo 'yar takarar shugabancin kasa a Faransa. © RFI/Pierre-René Worms
Talla

'Yar siyasa Anne Hidalgo Aleu wadda tsohuwar magajin birnin Paris ce kuma mace ta farko da ta taba rike mukamin, bayanai sun ce an haife ta ne a ranar 19 ga watan yunin shekarar 1959 a birnin San Fernando na Spain inda iyayenta suka yi hijira da ita a shekarar 1961 ta na da shekaru 2 a duniya.

Tsakanin shekarar 1997 zuwa 2002 Hidalgo ta yi aikace aikacen gwamnati da na hukumomi masu zaman kansu da dama ciki har da bayar da gagarumar gudunmawa wajen tsara dokokin da ke tabbatar da daidaiton jinsi Faransa.

A shekarar 2001 ne Hidalgo ta bi sahun kakanta wanda tsohon dan gwagwarmaya ne kuma dan siyasa a jam'iyyar Socialist can a Spain inda ta shiga harkokin siyasa gadan-gadan, ta hanyar tsayawa takarar neman shugabanci a zaben yanki tare da nasara a sassa 15 da jumullar kashi 26.5 na yawan kuri'un da aka kada a zagayen farko, wanda kuma ya bude mata hanyar ci gaba da gwagwarmayar siyasa.

A ranar 28 ga watan yunin shekarar 2020 ne aka zabi Anne Hidalgo a matsayin magajin garin Paris, bayan da ta lashe kashi 48.5 na zaben da aka yi.

A watan disamban shekarar 2020 kuma, gwamnatin Faransa ta ci tarar Hidalgo biyo bayan zaban mata 11 daga cikin 16 a majalisar zartaswa, matakin da ya sabawa kundun tsarin mulkin kasar na zaban fiye da kashi 60 na jinsi daya a shugabanci.

A watan Yunin 2021 ne ta sanar da aniyarta ta tsayawa takarar neman kujerar shugabancin Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.