Isa ga babban shafi

Zaben Faransa: Tarihin Nicolas Dupont-Aignan na jam'iyyar Debout la France

Nicolas Dupont-Aignan, wanda a wasu lokutan ake kira da NDA, dan siyasar Faransa ne da ya shahara tun daga shekarar 2008 a matsayin shugaban karamar jam'iyyar Debout la France, wadda a yanzu yake yi wa takarar kujerar shugabancin kasarsa.

Nicolas Dupont-Aignan dan takarar kujerar shugabancin kasar Faransa a karkashin jam'iyyar Debout la France.
Nicolas Dupont-Aignan dan takarar kujerar shugabancin kasar Faransa a karkashin jam'iyyar Debout la France. RFI
Talla

Nicolas Dupont dan jam'iyyar UMP ne har zuwa watan Janairun shekarar 2007, daga bisani kuma ya kafa kafa jam'iyyar Debout la France DLF a takaice a cikin Nuwamban 2008, wadda aka rika kira da sunan Debout la République har zuwa watan Oktoba na 2014.

Ya tsaya takarar neman shugaban kasar Faransa a shekarun 2012 da kuma 2017, inda ya goyi bayan Marine Le Pen da ta zo ta biyu, a zagaye na biyu na zaben shekarar ta 2017.

An haifi Nicolas Dupont-Aignan a ranar 7 ga Maris cikin shekarar 1961, a birnin Paris, da ga mahaifiyrasa Colette Aignan, da kuma Jean-Louis Dupont, tsohon sojan da ya fafata yakin duniya na biyu, wanda kuma ya tsere daga sansanin fursuna na Jamus.

Dupont-Aignan na da shaidar karatun digiri a fannin nazarin kimiyyar siyasa a shekarar 1982, ya kuma sami lasisin lauya a 1984.

Ya kuma fara rike mukaman siyasa da matsayin mai kula da harkokin gwamnati, inda yayi aiki a ma’aikatu da dama, ciki har da na Ministan Ilimi da Muhalli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.