Isa ga babban shafi
Amurka-Poland

Amurka za ta tura karin dakaru 3,000 Poland

Amurka ta ce za tya aike da karin dakaru dubu 3 zuwa Poland don kara wa kawayenta na NATO kwarin gwiwa a daidai lokacin da fargabar Rasha za ta mamaye Ukraine ke ci gaba da karuwa.

Wasu dakarun Amurka
Wasu dakarun Amurka © HO / SANA / AFP
Talla

Tun a karshen watan Janairu ne aka sanya dakarun  na musammana a cikin shirin ko-ta-kwana, bayan da shugaba Joe Biden ya bukaci haka.

Wani babban jami’i a ma’aikatar tsaron Amurka ya ce dakarun za su bar sansaninsu a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, kuma za su sauka Poland ne a cikin mako mai zuwa.

Wadannan dakaru  za su hade ne da 2000 da aka sanar da isarsu Poland a ranar 2 ga watan Fabrairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.