Isa ga babban shafi
Chile

An zabi shugaba mafi karancin shekaru a tarihin Chile

Kasuwar hannayen jari ta kasar Chile da kudin kasar peso sun yi galaba aka dalar Amurka, bayan da Gabriel Boric ya zama zababben shugaban kasa mafi karancin shekaru a tarihin kasar jiya Lahadi.

Zababben shugaban Chile Gabriel Boric.
Zababben shugaban Chile Gabriel Boric. AFP - MARTIN BERNETTI
Talla

Wannan dai wata gagarumar nasara ce ta ba zato ba tsammani  da matashin shugaban ya samu kan abokan hamayyarsa masu tsananin tsatssauran ra’ayi.

Sabon zababben shugaban kasar Gabriel Boric ya sha alwashin fadada 'yancin bil adama da kuma inganta walwalar jama’ar  kasar.

Sabon shugaban dai ya fuskanci suka sosai daga abokan hamayya, inda suke masa kallon dan gurguzu, a yakin neman zabe mai cike da rudani, Boric ya zama shugaban kasa mafi karancin shekaru a Chile da kusan kashi 56 na kuri'un da aka kada, idan aka kwatanta da kashi 44 na abokin hamayyarsa Jose Antonio Kast.

Wani abin mamaki shine abokin hamayyarsa wato Jose Antonio Kast, na masu ra’ayin rikau tuni ya taya zababben shugaban murna a shafin Twitter tun ma kafin a sanar sakamakon karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.