Boric mai shekaru 35 ya lashe zaben shugaban kasar Chile
Hukumar zabe a kasar Chile ta bayyana Gabriel Boric mai shekaru 35 a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar, abinda ya sanya daruruwan magoya bayan sa gudanar da bukukuwa a titunan birnin Santiago.
Wallafawa ranar:
Boric ya samu kashi 56 na kuri’un da aka kada, yayin da abokin karawar sa Antonio Kast ya samu kashi 44, kuma tuni ya amsa shan kayen zaben.
Masu bikin murnar nasarar sun yi ta amfani da kayan wasan wuta da rawa akan tituna domin bayyana farin cikin su.
Shugaban ‘Yan adawar kasar Kast da ya jagorancin kawancen da ya hada da na ‘yan ra’ayin rikau ya taya Boric murnar nasarar da ya samu.
Kast yace daga yau Boric ya zama zababben shugaban kasar Chile saboda haka ya dace kowa ya mutunta shi da bashi goyan bayan da ya bukata domin sanya kasar a gaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu