Isa ga babban shafi
Chile

Coronavirus: An killace rabin 'yan majalisar dattijan kasar Chile

Ma’aikatar lafiyar Chile ta sanar da killace rabin ‘yan majalisun zauren dattijan kasar mai kujeru 50, da kuma karin ministoci 2, bayan da suka yi mu’amala da wasu abokan aikinsu da gwaji ya tabbatar sun kamu da cutar coronavirus.

Wasu jami'an lafiya sanye da kayan samun kariya da cutar coronavirus, a wajen babban asibitin birnin Santiago, dake kasar Chile. 18/5/2020.
Wasu jami'an lafiya sanye da kayan samun kariya da cutar coronavirus, a wajen babban asibitin birnin Santiago, dake kasar Chile. 18/5/2020. AFP / MARTIN BERNETTI
Talla

Cikin sanarwar da suka fitar ta shafinsu na twitter, ministan kudi Ignacio Briones da kuma shugaban ma’aikatan gwamnati Felipe Ward sun ce gwajin farko ya nuna basa dauke da cutar, sai dai za su cigaba da killace kansu, har sai gwaji na 2 ya nuna basu kamu ba.

A halin da ake ciki, adadin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Chile ya kai akalla dubu 46, daga cikinsu kuma 478 sun mutu, abinda ya sanya gwamnati killace daukacin babban birnin kasar Santiago, la’akari da cewar kashi 80 na wadanda suka kamun a birnin suke.

A larabar makon da ya gabata, mutane 60 suka kamu da cutar coronavirus a rana 1 cikin kasar ta Chile, duk da cewar ta shafe wata guda da rabi karkashin dokar hana fita, domin dakile yaduwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.