Isa ga babban shafi
Pandora Papers

Chile ta fara binceken shugaban kasar kan zargin Rashawa

Ofishin mai gabatar da kara na kasar Chile ya bude bincike kan Shugaba Sebastian Pinera kan sayar da kamfanin hakar ma'adinai ta wani kamfani mallakar 'ya'yansa, wanda ya bayyana a cikin tonon sililin Pandora Papers.

Shugaban kasar Chile Sebastian Pinera.
Shugaban kasar Chile Sebastian Pinera. JAVIER TORRES AFP/File
Talla

A cewar Marta Herrera, shugaban sashin yaki da cin hanci da rashawa a ofishin mai gabatar da kara na gwamnati, Babban Lauya Jorge Abbott ne ya fara binciken bayan bayanan Pandora sun bayyana sayar da kamfanin hakar ma'adinai na Dominga da wani kamfani "mai alaka da dangin shugaba Pinera,"

Shugaba Pinera dai ya yi watsi da zargin yana mai cewa tuni aka wanke shi daga duk wani laifi a binciken shekarar 2017.

Batun sayar da kamfanin ma'adinan ga ɗaya daga cikin manyan abokan Pinera ya fara ne tun a shekarar 2010, a lokacin shugabancin sa na baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.