Isa ga babban shafi
Zaben Jamus

Jam'iyyar adawa ta SPD ta samu nasara kan CSU mai mulki

Sakamakon kuri’un da aka kada a zaben kasar Jamus a ranar Lahadi, ya nuna cewar Jam'iyar SPD ta masu sassaucin ra’ayi, ta sha gaban jam’iyyar shugaba mai barin gado Angela Merkel ta CSU mai ra'ayin mazan jiya da karamar tazara.

Dan takarar jam'iyyar adawa ta kuma Ministan Kudi Olaf Scholz.
Dan takarar jam'iyyar adawa ta kuma Ministan Kudi Olaf Scholz. REUTERS - WOLFGANG RATTAY
Talla

A yau Litinin Jamus ta tsinci kan ta cikin wani yanayi na rashin tabbas a fagen siyasa bayan da jam'iyar Social Democrat ta yi nasara a babban zabe, said ai nasarar ba ta bata damar kafa gwamnati ba kai tsaye, tilas sai ta nemi kawancen wasu jam’iyyun, saboda kankanuwar tazarar da ta baiwa  CSU mai ra'ayin mazan jiya ta shugabar gwamnati mai barin gado Angela Merkel.

Sakamakon da ya bayyana dai ya nuna dan takarar jam’iyyar Social Democrats ta SPD wato Ministan Kudi Olaf Scholz na kan gaba da kashi 25.7 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da Armin Laschet dan takarar Christian Democrats CSU mai mulki ke biye da su kusan kashi 24.1 na kuri’un da aka kada.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da dan takarar jam'iyya mai mulki ta CSU Armin Laschet.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da dan takarar jam'iyya mai mulki ta CSU Armin Laschet. REUTERS - WOLFGANG RATTAY

Jam'iyyar Green ce dai ta zo ta uku wajen yawan kuri’u a zaben na Jamus da kashi 14.8 cikin dari.

Yayin da tsokaci kan zaben da aka yi, Dan takarar CSU Armin Laschet, mai shekaru 60, ya dauki alhakin rashin karsashin da jam’iyyarsa ta yi tare da alkawarin daukar matakan gyara

Yayin da shi kuma dan takarar SPD Olaf Scholz ya ce. kawancen jam’iyyun CDU da CSU ba kawai sun rasa kuri'unsu ba ne, sako suka samu daga daga 'yan kasa na cewar - bai kamata su ci gaba da jagorantar gwamnatin Jamus ba said ai su koma ‘yan adawa.

Dangane da rashin tabbas din da ake ganin siyasar Jamus ta shiga kuwa, Scholz ya ce babu wata matsala da za ta kunno kai a siyasar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.