Isa ga babban shafi
Zaben Jamus

Jamusawa sun kada kuri'a a zaben magajin Merkel

Miliyoyin Jamusawa sun jefa kuri'a a zaben Jamus da ke kawo karshen shugabancin gwamnatin kasar da Angela Merkel ta shafe shekaru da dama tana yi.

Mutane sun yi layi a gaban wata rumfar zabe a gundumar Moab da ke birnin Berlin a kasar Jamus. Ranar Lahadi 26 ga Satumba, 2021.
Mutane sun yi layi a gaban wata rumfar zabe a gundumar Moab da ke birnin Berlin a kasar Jamus. Ranar Lahadi 26 ga Satumba, 2021. AP - Michael Probst
Talla

Zaben dai shi ne irinsa na farko tun lokacin da gabashi da kuma yammacin Jamus suka sake hadewa a shekarar 1990, wanda kuma shugabar gwamnatin kasar mai barin gado Angela Merkel ba za ta shiga takara ba, bayan shafe shekaru 16 kan mukamin na ta.

Sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka yi ana gaf da zaben na Jamus, ya nuna cewar har yanzu jam'iyyar Social Democrat ta SPD ke kan gaba wajen karbuwa, fiye da jam’iyyar Merkel ta Christian Democratic Union CDU da kuma wadda suke kawance ta Christian Social Union CSU.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ta baya bayan nan ta sanya  zaben shugabancin gwamnatin ta Jamus zama mai zafi tsakanin bangaren masu hammaya da masu mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.