Isa ga babban shafi
jAMUS - RASHA

Merkel ta bukaci Putin ya saki jagoran adawarsa dake tsare a kurkuku

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci shugaba Vladimir Putin na Rasha da ya saki abokin hamayyarsa na siyasa Alexei Navalny. Merkel dai ta yi wannan kira ne a lokacin da take ganawa da shugaba Putin a wannan Juma’a a birnin Moscow.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Rasha Vladimir Poutine yayin wata ganawa a Rasha 2/5/2017.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Rasha Vladimir Poutine yayin wata ganawa a Rasha 2/5/2017. REUTERS/Alexander Zemlianichenko
Talla

Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da dangantaka ke kara yin tsami tsakanin Rasha da kasashen yamma, kan batutuwa da dama, ciki har da batun garkame jagoran 'yan adawar kasar, Alexei Navalny.

Mukarraban Merkel sun bayyana cewar, ba kuskure bane ziyarar shugabar Jamus mai barin gado zuwa Moscow a dai-dai lokacin da ake tunawa da zagayowar ranar da aka sanyawa Navalny guba.

A wani bangare na ganawar da aka yada a gidan talabijin, Merkel ta ce, ‘’Duk da cewar muna da sabani a tsakanin mu dan gane da wasu batutuwa, akawai bukatar mu tattauna da juna dan samar da mafita’’.

Shugabar gwamnatin ta Jamus ta kara cewa, ‘’za mu tattauna kan wasu batutuwa, ciki har da, halin da ake ciki a Afghanistan bayan ‘yan Taliban suka kwace mulkin kasar, sannan ta ce akwai bukatar ci gaba da tattaunawa tsanakin Rasha da Ukraine don warware sabanin da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.