Isa ga babban shafi

Kasashen duniya sun bukaci Rasha da ta gaggauta sakin Navalny

Kasashen Yammacin Duniya na ta kira ga gwamnatin Rasha da ta yi gaggawar sakin jagoran adawar kasar Alexei Navalny dake tsare a ofishin‘ yan sanda a Moscow bayan kama shi da aka yi a filin jirgin saman kasar jim kadan bayan sauka daga Jamus.

Jagoran adawar Rasha Alexei Navalny
Jagoran adawar Rasha Alexei Navalny AP Photo/Pavel Golovkin
Talla

Yanzu haka babban mai sukar Shugaba Vladimir Putin na ci gaba da jiran ganin lauyoyinsa sa’o’i bayan tsare shi da akayi a filin tashi da saukar jiragen saman Moscow, jim kadan bayan dawowarsa daga kasar Jamus inda yake murmurewa bayan wani harin guba da yayi kusan hallaka shi.

Tsarewan da 'Yan sanda sukayiwa Navalny, yaci gaba da haifar da tofin Allah tsine daga kasashen ketare masamman Yammacin Turai, da masu fafutuka da suka bukaci Kremlin da ta yi gaggawar saki shi.

Ministan Harkokin Wajen Jamus Heiko Maas ya ce, sun kasa fahimtar wannan lamari, inda ya bukaci hukumomin Rasha da suyi gaggawar sallamar Navalny.

A cewar Maas, Navalny "ya yanke shawarar komawa Rasha saboda yana ganin gidan sane kuma inda yake fafutukar sa ta siyasa.

Wani na kusa Navalny ya bayyana cewar, ana tsare da dan na adawar ne a garin Khimki da ke wajen birnin Moscow, inda ake saran tawagar lauyoyinsa su ziyarce shi.

Kasar Amurka da Tarayyar Turai da gwamnatocin EU da dama da Canada da wani babban mai taimaka wa zababben Shugaban Amurka Joe Biden, duk sun bukaci sakin Navalny, yayin da wasu daga cikin kasashen Turai ke neman a sake sanya wa Rasha takunkumi.

Kungiyoyin kare hakkin bi’adama irinsu Amnesty International sun bi sahun kasashen wajen bukatan ganin Rasha ta saki babban mai sukar gwamnatin shugaba Vladimir Putin.

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Charles Michel ya ce tsare Navalny ba abin lamunta ne, yayin da ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ce kamun abin damuwa ce matuka.

Anata bangare Rasha ta bakin Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar, Maria Zakharova ta mayar da martani tana kashedi ga shugabannin kasashen waje cewa su mutunta dokokin kasa-da-ka tare da kira da su magance matsalolin kasar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.