Isa ga babban shafi
Faransa - Coronavirus

Faransawa dubu 170 sun sake yin zanga-zangar adawa da dokar yaki da Korona

Dubban mutane sun sake yin zanga-zanga a titunan Faransa don adawa da manufofin gwamnatin kasar kan rigakafin cutar Korona.

Masu zanga-zangar adawa da sabuwar dokar Korona a Faransa
Masu zanga-zangar adawa da sabuwar dokar Korona a Faransa © AFP/Stéphane de Sakutin
Talla

Zanga-zangar da ta shiga mako na 6 a jiya Asabar na ci gaba da gudana ne a yayin da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka bayyana damuwa kan shigar masu nuna kyamar Yahudawa a cikin gangamin 'yan adawar.

Masu adawa da gwamnatin Faransar sun yi ta A-wadai da dokar tilastawa mutane yin allurar rigakafi da kuma nuna shaidar gwajin Korona, wadda suka bayyana a matsayin tauye hakkokin wadanda ba su karbi riga-kafi cutar ba.

Ma'aikatar cikin gidan Faransa ta ce adadin mutanen da suka fita zanga-zangar ta ranar Asabar ya kai kusan dubu 175,000, ciki har da akalla dubu 14 da 700 a birnin Paris kadai.

Kimanin mutane dubu 200 ne suka yi tattakin adawa da shirin gwamnatin shugaba Emmanuel Macron kan annobar Korona a karshen makon da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.