Isa ga babban shafi
Faransa

Dubban masu adawa da dokokin Korona sun yi tattaki a sassan Faransa

Masu zanga-zanga fiye da dubu 200,000 sun yi tattaki a sassan Faransa a yau Asabar, domin adawa da tilasta musu nuna shaidar karbar allurar rigakafin Korona ko kuma ta gwajin cutar da Shugaba Emmanuel Macron ya kafa don gaggauta kawo karshen annobar.

Masu zanga-zangar adawa da sabuwar dokar yaki da annobar Korona a Paris.
Masu zanga-zangar adawa da sabuwar dokar yaki da annobar Korona a Paris. AP - Adrienne Surprenant
Talla

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Faransa ta ce jimillar mutane dubu 214 da 845 ne suka gudanar da zanga-zangar ciki har da kusan dubu 14 a birnin Paris kadai.

Mako na biyar kenan da ake zanga-zangar adawa da dokar tilastawa mutane gwaji ko yin allurar rigakafin korona kafin samun walwalar yau da kullum ciki har da shiga gidajen saida abinci da kuma wuraren shan gahawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.