Isa ga babban shafi
Faransa - Coronavirus

Shaidar bogi ta gwajin korona da rigakafinta sun mamaye Faransa

Kasuwar sayar da katin shaidar karbar allurar rigakafin covid-19 da na gwajin ta na bogi, ta bude a Faransa bayan da wasu al’ummar kasar ke cin amincewa da karbar rigakafin cutar, duk da kiraye-kirayen gwamnati na ganin jama’a sun bayar da hadin kai wajen yaki da cutar.

Wani dake dauke da takardun shaidar allurar rigakafin korona a Faransa 12/02/21.
Wani dake dauke da takardun shaidar allurar rigakafin korona a Faransa 12/02/21. AFP - JENS SCHLUETER
Talla

Bayanai sun ce tun bayan da gwamnatin kasar ta janye dokar takaita walwalar jama’a ne mutane ke ci gaba da tururuwar neman katin shaidar basa dauke da cutar na bogi ta hanyar biyan kudi masu yawa da nufin samun damar shiga cikin hada-hadar jama’a.

A wani yunkuri na tilastawa jama’a karbar rigakafin cutar ta Covid-19, gwamnatin ta Faransa ta tilastawa jama’a ko dai nuna shaidar allurar ko kuma nuna katin shaidar gwaji a ilahirin gidajen abinci da wuraren shakatawa har ma da jiragen kasa wanda zai tabbatar mutanen basa dauke da cutar.

Sai dai matakin na gwamnati ya bayar da damar budewar wata kasuwar bayan fage a shafin Intanet ta yadda Faransawan ke biya a basu shaidar basa dauke da cutar ba tare da gwaji ba, don samun damar shiga cikin hada-hadar jama’a.

Duk da wani bincike da ke nuna Faransawa na goyon bayan matakin gwamnatin na tilasta karbar rigakafin amma bangaren adawa ya shafe tsawon makwanni 5 a jere yana jagorantar zanga-zangar adawa da matakin.

Tuni gwamnati ta gano wasu shafukan tallata katunan shaidar ko dai na rigakafin ko kuma na gwajin mai dauke da ba a dauke da cutar.

Duk da kasancewar rigakafin kyauta a Faransa, mutanen na biya yuro 350 don samun sakamakon na bogi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.