Isa ga babban shafi
Turai-Afrika

EU za ta tallafawa matalautan kasashen da yuro miliyan 250 don yakar yunwa

Kungiyar tarayyar turai ta yi alkawarin karin Euro miliyan 250 a matsayin tallafi ga kasashen Afirka, Afghanistan da Venezuela, domin shawo kan matsalolin yunwa, kudaden da kungiyar ta ce wani bangare ne na kasafinta da ta ware daban da nufin tallafawa mabukatan kasashe.

Shugabar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.
Shugabar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen. AP - John Thys
Talla

Matakin na EU na zuwa gabanin taron kungiyar kasashe 7 mafiya karfin tattalin arziki na duniya da zai gudana a Birtaniya cikin makon nan.

Shugabannin manyan kasashe na ci gaba da fuskantar kiraye-kiraye don cika alkawuran da aka yi na samar da biliyoyin kudi da nufin magance matsalar ta yunwa da ke barazana ga kananun kasashe.

Sai dai matakin na EU na zuwa a dai dai lokacin da Firaministan Birtaniya Boris Johnson mai masaukin baki a taron na G7 ke fuskantar babbar suka game da shirin rage kasafin kudin kasar sa na tallafin da ta saba baiwa kasashe masu rauni.

EU ta ce tallafin na ta na yuro miliyan 250 za su taimaka wajen wadata matalauta kasashe da cutar covid-19 ta sake jefawa a matsalar kamfar abinci.

A watan Maris din da ya gabata ne Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutane miliyan 34 na gab da fuskantar tsananin yunwa a kasashe 20 galibi matalauta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.