Isa ga babban shafi

Coronavirus ta kashe mutane 475 a Italiya a kwana daya

Adadin wadan da suka mutu a fadin duniya sanadiyar cutar coronavirus ya haura 8,000,yayin da kasar Italiya da Iran suka fitar da alkaluman dake cewa fiye da mutane 500 suka rasa rayukan su a cikin sa’o’i 24 a kasashen.

Allon da ke nuna alamun kariya daga kamuwa da cutar coronavirus a filin jiragen saman kasar Italiya
Allon da ke nuna alamun kariya daga kamuwa da cutar coronavirus a filin jiragen saman kasar Italiya REUTERS/Yara Nardi
Talla

Alkaluman kasar Italiya dangane da mace macen cutar coronavirus suna matukar firgirtawa domin kuwa a cikin sa’o’I 24 mutane 475 suka mace wanda yasa adadin mamatan 2,978, wadan da suka kamu da cutar kuwa yawan su ya haura dubu 35,713, adidan mafi yawa da aka taba gani a duniya tun bayan bullar cutar a kasar China karshen shekarar bara.

Kasar Iran ne ta fitar da alkaluman muatne 147 suka mace a cikin sa’o’I 24 wanda yasa adadin wadanda suka mace a kasar zuwa 1,135.

Wadanda suke fama da cutar a Spaniya ta kai 13,700 adadin da ya karu da 2,538 daga ranar Talata.

Kasar Turkiya da Bangladesh da Moldova da Burkina Faso duk a karon farko sun sanar da macewar mutum guda guda.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.