Isa ga babban shafi
Italiya

Italiya ta killace kashi 1 bisa 4 na al'ummarta saboda Coronavirus

Gwamnatin Italiya ta dauki matakin killace kashi 1 bisa 4 na daukacin al’ummar kasar, bayanda a safiyar yau ta dakatar da shige da fice a yankin arewacin kasar, don dakile yaduwar annobar murar Coronavirus dake barna a kasar.

Wani sashin birnin Milan na Italiya bayan takaita zirga-zirga saboda annobar Coronavirus.
Wani sashin birnin Milan na Italiya bayan takaita zirga-zirga saboda annobar Coronavirus. Reuters/Guglielmo Mangiapane
Talla

Matakin killace arewacin kasar ta Italiya da ya shafi sama da mutane miliyan 15, zai ci gaba da wanzuwa har ranar 3 ga watan Afrilun dake tafe, inda dole sai da kwakkwaran dalili za a baiwa mutane damar shiga yankin arewacin Italiyan, ciki har da biranen Venice da Milan.

A wani matakin kuma gwamnatin Italiyan ta rufe baki dayan gidajen Sinima, filayen wasannin kalankuwa da kuma gidajen adana kayan tarihi dake kasar, duk dai kan annobar murar ta Coronavirus.

Jami’an lafiya sun ce yanzu haka annobar ta Coronavirus ta halaka mutane sama da 200, kusan dubu 6 kuma sun kamu a kasar ta Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.