Isa ga babban shafi
Venezuela

Rasha ta gargadi Amurka kan tsoma baki a rikicin Venezuela

Rasha ta bukaci Amurka ta kawo karshen tsoma baki kan rikicin siyasar Venezuela, lura da yadda take ci gaba da matsin lamba kan shugaba Nicolas Maduro, bayan ‘yan adawa sun gaza cimma muradunsu na kifar da gwamnatinsa.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov.
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov. REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

A yayin ganawa da takwaransa na Venezuela a birnin Moscow, Ministan Harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya yi kira ga Amurka da kawayenta su yi watsi da mummunan shirinsu akan Venezuela, sannan kuma su mutunta dokokin kasa da kasa.

Lavrov ya ce, Amurka na yi wa Venezuela matsin lamba ne don ganin ta kifar da halastaciyar gwamnatin kasar.

A lokacin da yake jawabi, Ministan Harkokin Wajen Venezuela, Jorge Arreaza ya mika godiya ta musamman ga Rasha saboda goyon bayan da take nuna wa gwamnatin Maduro, yana mai cewa, alakar da ke tsakanin kasashen biyu ta dada karfafa.

Rasha da ta kasance babbar mai bai wa Venezuela rance, ta karfafa goyon bayanta ga gwamnatin Maudro ta hanyar aikewa da gomman sojoji zuwa kasar, yayinda ta yi watsi da ikirarin jagoran ‘yan adawar kasar, Juan Guaido na zama halastaccen shugaban kasa.

Sai dai a yayin mayar da martani, Sakataren Harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya nuna wa Rasha yatsa, in da ya bukace ta da ta fice daga batun Venezuela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.