Isa ga babban shafi
Venezuela

Ricikin siyasar Venezuela ya sake dagulewa

Rikicin Siyasar kasar Venezuela ya sake dagulewa, sakamakon ikrarin shugaban Yan adawa Juan Guaido cewar, wasu sojojin kasar sun yi masa mubayi’a, yayin da shugaba Nicolas Maduro ya bayyana matakin a matsayin wani yunkuri na juyin mulki, kuma yace daukacin shugabannin sojin kasar sun jaddada goyan bayan su a gare shi.

Wasu magoya bayan jagoran 'yan adawar kasar Venezuela Juan Guaido, yayin zanga-zangar adawa da shugaba Nicolas Maduro.
Wasu magoya bayan jagoran 'yan adawar kasar Venezuela Juan Guaido, yayin zanga-zangar adawa da shugaba Nicolas Maduro. REUTERS/Carlos Eduardo Ramirez
Talla

Colombia da ke makwabtaka da Venezuela ce ta soma tsokaci kan sabon salon da rikicin kasar ya dauka, Inda ta shafinsa na Twitter, shugaban Colombian Ivan Duque ya shawarci ‘yan Venezuela da dakarun sojin kasar su nuna turjiya ga mulkin kama karya na gwamnatin Maduro, zalika ya bayyana shirin kiran taron kasashen Latin na Kungiyar Lima kan halin da ake ciki.

Shi kuwa shugaban Bolivia Evo Morales amfani yayi da kakkausan harshe wajen sukar yunkurin juyin mulki a kasar ta Venezuela, tare da bayyana masu hannu a cikinsa a matsayin masu bin ra’ayin son zuciya na kasashen ketare.

Duk da cewa a baya Spain ta goyi bayan jagoran ‘yan adawar Venezuela Juan Guaido, a wannan karon, ta hau kujerar naki kan zabin yin juyin mulkin, kamar yadda shugaban Cuba Miguel Diaz-Canel ya bayyana a shafinsa na Twitter.

Kungiyar kasashen Turai EU kuwa, bayyana cewa tayi tana biye da abinda ke faruwa a kasar ta Venezuela ba tare da ta yi tsokaci akai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.