Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya nuna damuwa kan lalata kaburburan Yahudawa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sha alwashin samar da dokar da za ta hukunta wadanda ke da hannu a lalata kaburburan yahudawa, bayan ziyarar da ya kai ga wasu kaburbura kusan dari na yahudawan kasar a yau Talata wadanda aka yi rubutun batanci a jikinsu.

Ziyarar da Macron ya kai Makbartar Yahudawan da aka lalata kaburbura 96
Ziyarar da Macron ya kai Makbartar Yahudawan da aka lalata kaburbura 96 REUTERS/Vincent Kessler
Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda ya ziyarci makabartar da lamarin ya faru jim kadan bayan sanar da shi a yau Talata, ya ce Faransa za ta tashi tsaye don bayar da cikakkiyar kariya ga makabartun Yahudawan da ke kasar.

Akalla kaburbura 96 aka yiwa wasu rubutu na nuna kyama a wata makabartar yahudawa da ke gab da kan iyakar Faransar da kasar Jamus, wanda kuma shi ne irinsa na biyu cikin kasa da watanni 3 da aka fuskanta a Faransar.

A ziyarar da ya kai makabartun Macron ya alakanta masu lalata kaburburan yahudawan da marasa kishin kasa, inda ya rika dora furanni kan kaburburan da nufin girmamawa.

Lalata kaburburan dai na zuwa ne sa’o’I kalilan gabanin fara wani gangamin yaki da nuna wariya da aka tsara gudanarwa a sassan kasar ta Faransa.

Tuni dai ministan shige da Fice na Isra’ila Yoav Gallant ya ce matakin zai tilasta kwaso yahudawan da ke Faransar da basu cikakken tsaro a Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.