Kungiyar Yahudawa ta bukaci shugaban Philippines ya nemi afuwarta
Kungiyar Yahudawa ta Duniya yi kakkausar suka ga kalaman shugaban Philippines Rodrigo Duterte, wanda ya kamanta yakin da yake da masu tu’ammuli da miyagun kwayoyi a kasarsa da kisan kare dangin da Gwamnatin Nazi karkashin Adolf Hitlar ta yiwa Yahudawa.
Wallafawa ranar:
A baya Duterte ya furta kalaman cewa zai yi farin cikin zai kashe masu tu’ammali da muggan kwayoyi a kasar, kamar yadda Hitlar a kashe Yahudawa a lokacin mulkinsa a Jamus.
Shugaban kungiyar Yahudawa na Duniya Ronald S. Lauder, ya bukaci shugaban na Philippines ya janye kalamansa tare da neman afuwa.
Kawo yanzu dai sama da mutane 3000 aka kashe a Philippines wadanda aka zarga da ta’ammuli da muggan kwayoyi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu